IQNA

An Hana Duk Wani Take Na Bangaranci A Tattakin Arbaeen A Iraki

23:53 - October 17, 2019
Lambar Labari: 3484161
Bangaren kasa da kasa, Mahukunta a Iraki sun hana duk wani take na nuna bangaranci a tattakin arbaeen

Kamfanin dillancin labaran iqna, Jawad Gazali shugaban majalisar lardin Najaf a kasar Iraki ya sanar da cewa, ba za su lamunce duk wani mataki da wasu masu tattali za su dauka na yin taken nuna bangaranci ko aibanta wani bangare a lokacin tattaki ba.

Ya ce wannan mataki na gwamnatin raki ne, kuma an tanadi dokoki na hukunta duk wanda ya sabawa wannan doka, ba tare da la’akari da cewa shi dan Iraki ne ko dan kasar waje ba.

Haka nan kuma Gazai ya yi ishara da cewa, daga cikin manufofin  tattaki akwai raya hadin kan al’ummar msuulmi da yin aiki tare da juna domin daukaka tafarkin addinin muslunci, wanda shi ne tafarkin manzon Allah, wanda kuma a kan wannan tafarki ne Imam Hussain tare da wadanda suke tare da shi suka yi shahada.

Wannan mataki na zuwa ne sakamakon yadda wasu masu tsatsauran ra’ayi da jahilci sukan rera take a lokacin tattakin arbaeen wanda bai dace da koyarwar iyalan gidan manzon Allah ba, kuma hakan ya sabawa manufar tattakin.

3850654

 

 

captcha