IQNA

An Sake Dawo Da Dokar Hana Zirga-Zirga A Wasu Yankunan Kashmir Ta India

21:52 - October 18, 2019
Lambar Labari: 3484167
Bangaren kasa da kasa, mahukunta yankin Kashmir da Jamo a kasar India sun sake da dokar hana zirga-zirga a wasu yankuna.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin Autoclock India cewa, mahukunta yankin Kashmir da Jamo a kasar India sun sake da dokar hana zirga-zirga a wasu yankuna da suka hada da Sringar.

Mahukuntan yankin sun ce an dauki wannan mataki ne musamman a wannanyanki na Sringar, domin tabbatar da tsaro da kuma doka da oda, domin kauce wa yunkurin wasu na tunzura jama’a da su fito domin yin bore ga gwmnatin India.

Tun a ranar 5 watan Agustan wannan shekara ne dai firayi ministan kasar India ya sanar da cewa ya soke dokar da ta baiwa yankin Kashmir kwarya-kwaryan cin gishin kai har illa masha’allahu.

A cikin kundin tsarin mulkin kasar India doka ta 370 ta baiwa yankin Kashmir iko gudanar da komai a cikin ‘yanci, da hakan ya hada da zaben shugaba yankin da ministocinsa da ‘yan majalisar dokoki da sauransu.

Amma dokar ta kebance batun siyasar harkokin waje da kuma tsaro, wanda hakan ya shafi gwamnatin India ne kai tsaye.

3850788

 

 

captcha