IQNA

An Bude Bangaren Nazarin Ilmin Kur'ani A Jami'ar Yemen

23:45 - July 19, 2017
Lambar Labari: 3481716
Bangaren kasa da kasa, an bude tsangayar koyar da ilimin kur'ani a jami'ar Hadra maut da ke cikin gundumar Aden a kasar Yemen.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an bude wannan tsangaya ne da nufin kara fadada kwasa-kwasan ilmomin kur'ani mai tsarki a jami'oi .

Byanain ya ce shirin zai fara ne daga wannan shekara ta 2017 zuwa ta 2018, inda yanzu haka an fara rijistar dalibai wadanda suke son zabar kwas din ilimin kur'ani mai tsarki.

Kasar Yemen dai na daga cikin kasashen larabawa da suke mayar da hankali matuka wajen lamurran da suka shafi kur'ani mai tsarki da hadisi, duk kuwa da cewa kasar dai tana fama da matsalolin da aka haddasa mata na yaki, wanda hakan ya jawo koma baya matuka a wasu yankunan da 'yan mamaya suke kaddamar da hare-hare.

Shirin da jami'ar take da shi dai zai mayar da hankali ne wajen dandake ilimomin kur'ani mai tsarki, da kuma fitar da fagage da za aiya yin karatun kwarewa akansu duk a cikin ilmomin kur'ani a wannan tsangaya.

3620658


captcha