IQNA

Taron Tattaunawa Tsakanin Mabiya Addinai A Birnin Manchester

17:44 - July 25, 2017
Lambar Labari: 3481734
Bangaren kasa da kasa, An gudanar da wani taron tattaunawa tsakanin jagororin mabiya addinai a birnin Manchester da ke kasar Ingila, domin kara samun damar fahimtar juna a tsakanin dukkanin mabiya addinai.
Kamfanin dilllancin labaran iqna ya habarta cewa, taron wanda aka baiwa take sulhu da hadin kai tsakanin al'umma, ya samu halartar jagororin mabiya addinai daban-daban, da suka hada da muslunci, kiristanci, yahudanci, buda, hindus da sauransu, inda bangarorin suka bayyana mahanrsu a kan muhimman abubuwan da ya kamata dukkanin mabiya addinai suka rika yin la'akari da su a cikin rayuwa ta zamantakewa da sauran mutane.

Wannan taro dai ya gudana ne domin yin bita  dangane da abubuwan da suke jawo tsatsauran ra'ayi a cikin addini wanda har ya kan kai wasu ga aikata muggan ayyuka da sunan addini, duk da cewa an fi saurin danganta wasu mabiya addinin muslunci da hakan, amma akwai wasu daga cikin sauran addinai da suke aikata laifuka na ta'addanci da sunan addini.

Musulmin da suka halarci wurin dai sun yi karin haske ga mahalarta wurin da cewa, addinin muslucni addini ne na zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai da ma al'adu, kuma masu aikata ta'addanci da sunan muslunci ba suna wakiltar addininmuslunci ko musulmi ba ne.

3622892


captcha