IQNA

Zaman Gaggawa Na Kwamitin Tsaro Kan Batun 'Yan Rohingya

23:58 - September 12, 2017
Lambar Labari: 3481888
Bangaren kasa da kasa, A wani lokaci, yau Talata ne kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani zama domin tattauna batun 'yan Rohingyas.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Kwamitin ya amunce yin zamen ne bisa bukatar kasashen Birtaniya da kuma Suiden domin tattauna batun na musulmin Rohingyas a Myammar.

Wannan dai na zuwa ne bayan babban jami'in MDD mai kare hakkin bil adama, Zeid Ra'ad Al Hussein,ya danganta kisan da akewa musulmai 'yan kabilar Rohingyaa kasar ta Myanmar da na kare-dangi.

A ranar Lahadi data gabata mayakan dake fafatukar kare 'yan Rohingyas sunsanar da tsagaita wuta, saidai gwamnatin Myammar ta ce bata tattaunawa da 'yan ta'adda.

A wata sanarwa data fitar gwamnatin taAung San Suu Kyi ta ce tana ci gaba da goyan bayan sojojin kasar, aman ta jaddada cewasojojin sun samu umurninta na yin takatsan-tsan da kuma kaucewa taba fararen hula a cikin aikinsu na tabbatar da tsaro.

Saidai kuma a wani labarin babban hafsan sojin kasar ta Myammar ya ce babu 'yan Rohingyas a cikin tarihin kasar.

Kawo yanzu alkalummen da MDD ta fitar sun nuna cewa adaddin 'yan gudun hijira Rohingyas da suka tsallaka zuwa Bnagaladash ya haura dubu dari uku.

3640934


captcha