IQNA

An Raba Kayan Taimako na Iran Ga Musulmin Rohingya A Bangaladesh

23:21 - September 17, 2017
Lambar Labari: 3481905
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar bagaladesh sun bayar da damar raba dukkanin kayan taimako da Iran ta aike ga al’ummar Rohingya da ke gudun hijira.

Kamfanin dillancin labara iqna ya bayar da rahoton cewa, jami’an gwamnatin kasar bagaladesh sun bayar da damar raba dukkanin kayan taimako da Iran ta aike da suga al’ummar muuslmi ‘yan kabilar Rohingya da ke gudun hijira a kasar, tare da halartar Murtada Salimi.

Kayan da aka raba ya zuwa yanzu sun kai ton 40 wadanda suka hada da kayan abinci da kuma magunguna.

Kafin wanan lokacin mahukuntan Iran sun sanar da cewa an samu tsaiko ne aya aikewa da kayan zuwa gabar ruwan bangaladesh, sakamakon rashin bayar da damar raba su daga mahukuntan kasar, inda suka amince da hakan daga bisani.

An safke dukkanin kayan nea gabar rua da Kakas bazar na kasar bangaladesh, inda daga nan aka dauke su zuwa sasanonin ‘yan gudun hijira.

3643036


captcha