IQNA

Shekara Ta 2017 Ita Ce Mafi Muni Ga Kabilar Rohingya

23:40 - December 24, 2017
Lambar Labari: 3482232
Bangaren kasa da kasa, kwamitin ‘yan kabilar Rohingya mazauna nahiyar turai sun bayyana shekarar 2017 a matsayin shekara mafi muni ga dukkanin ‘yan kabilar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar quds Alarabi cewa, kwamitin ‘yan kabilar Rohingya mazauna nahiyar turai sun bayyana shekarar 2017 a matsayin shekara mafi muni ga dukkanin ‘yan kabilar ta Rohingya.

Bisa kididdiga da kungiyoyin kasa da kasa da suka hada da majalisar dinkin duniya suka fitar kan batun cin zarafi da ian gillar da aka yi ‘yan kabilar Rohingya a Myanmar, utane kimanin dubu 650 ne suka yi gudun hijira zuwa Bangaladash.

Haka nan kuma rahotanin sun tabbatar da cewa kimanin kashi 65 cikin na wannan kabila sun samu matsala ta tunani.

Kwamitin ya kirayi kungiyoyin kasa da kasa da kuma kasashen musulmi musamman da su taimaka ma wadannan mutane da suke fuskantar kisan kiyashi a kasarsu.

Kungiyar likitoci ta kasa da kasa ta tabbatar da cewa, fiye da mutane dubu ne ‘yan kabilar Rohingya sojojin gwamnatin Myanmar suka kasha, tare da yi wa dubban ‘yan mata fyade.

3675801

 

 

 

 

captcha