IQNA

Ana Shirin Mayar Da 'Yan Rohingya Zuwa Myanmar

16:53 - January 08, 2018
Lambar Labari: 3482279
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Bangaladesh na shirin fara kwashe dubban daruruwan 'yan kabilar Rohingya zuwa Myanmar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Arakan cewa, Muhammad Abu Kalam daya daga cikin manyan jami'an gwamnatin Bangaladesh yana cewa, yanzu haka sun shirin fara kwashe dubban daruruwan 'yan kabilar Rihingya zuwa Myanmar a cikin wannan mako.

Ya ce sun tattauna da mahukuntan Myanmar kan kan hakan, kuma tuni aka fara gudanar da cike fam a tsakanin dukkanin 'yan gudun hijira na kabilar Rohingya da suke zaune a cikin kasar Bangaladesh, inda suke ganin hakan a matsayin muhimmin lamari.

Da dama daga cikin 'yan gudun hijirar dai basa son komawa kasar tasu, sakamakon kisan gilla da aka yi musu tare da kashe dubbai daga cikinsu da wawushe musu kaddarori da kone musu musu dukiyoyi.

Jami'an tsaron gwamnatin Myanmar tare da 'yan addinin buda masu tsatsauran ra'ayi ne suka aikata hakan,  kamar dai yadda rahotanni na mjalaisar dinkin duniya da kuma na kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya suka tabbatar.

3679686

 

captcha