Kamfanin dilalncin labara iqna ya habarta cewa, cibiyar Imam Ali (AS) da ke birnin Vienna na kasar Ausria ta sanar da cewa, ta samar da wani sabon tsari na naura mai kwakwalwa wanda yake dauke da surat yasin da dukkanin abubuwan da suke da alaka da ita da suka hada da kira’a da kuma tafsirinta gami da bayanin falalolinta.
Cibiyar ta gudanar da wannan aiki ne musamman domin amfanin masu fahimtar harshen jamusanci, wada kuma za a iya samunsa a cikin matattarar fitar da shirye-shirye ta yanar gizo.
Haka nan kuma masu amfani da wayar salula da take da tsarin safke application a tsaron google play za su iya yin amfani da shi.