IQNA

Limamai A Tunisia Sun Ki Amincewa Da Daidaita Maza Da Mata A Gado

23:18 - January 05, 2019
Lambar Labari: 3483285
Bangaren kasa da kasa, limaman masallatai a kasar Tunisia sun ki amincewa da batun daidaita mata da maza a sha’anin gado.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, malaman masallatai daga sassa daban-daban na kasar Tunisia ne suka taru a birnin Tunis fadar mulkin kasar, domin nuna rashin amincewarsu da daftarin kudirin da ke neman a daidaita mata da maza kan sha’anin gano.

Muhammad saleh Rudaid mai magana da yawun gungun limaman ya bayyana cewa, a cikin kundin tsarin mulkin kasar Tunisia a fasali na 1, 6, 145, 146, an bayyana cewa, addinin muslunci shi ne addinin kasa a hukumance, kuma batun tsarin gado da ke cikin kur’ani shi ne tsarin da musulunci ya yi kuma ya yarda da shi, saboda haka saba ma wannan yana matsayin sabawa kundin tsarin mulkin kasar Tunisia ne a hukumance.

Tun a cikin bazarar shekarar da ta gabata ce shugaban kasar ta Tunisia Muhammad Sibsi kaid Baji ya gabatarwa majalisar ministoci da mahangarsa kan batun daidaita maza da mata a sha’anin gado, kuma majalisar ministocin ta amince da hakan, inda aka mika batun ga majalisar dokokin domin kada kuri’a a kansa.

A cikin ‘yan kwanaki masu zuwa ne dai ake sa ran majalisar dokokin kasar ta Tunisia za ta kada kuri’a kan wannan daftarin doka.

3778689

 

 

 

captcha