Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar Ukraine ta bayar da sanarwar cewa, tana shirin saka gudanar da wasu ayyuka na saka hannayen jari a Isra’ila, a kan haka za ta bude ofishin wakilci a birnin Quds, wanda zai zama a a matsayin karamin ofishin jakadancinta.
Bayanin ya ce baya ga birnin na Quds za a bude wasu ofisoshin na wakilci a wasu garuruwan da za su zama karkashin kulawar ofishin na birnin Quds.
Yesrael Katz ministan harkokin wajen Isra’ila ya yi lale marhabin da matakin na gwamnatin Ukraine.
A cikin wanann shekara da muke ciki daruruwan yahudawa ne suka yi hijira daga Ukraine zuwa Isra’ila, inda aka tsugunnar da su a matsugunnan yahudawa ‘yan share wuri zauna da ke kusa da yankin zirin Gaza.