IQNA

Sayyid Hassan Nasrullah:

Babu Gaskiya Kan Cewa Ana Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka / Na Yi Farin Cikin Faduwar Trump

14:37 - November 12, 2020
Lambar Labari: 3485358
Tehran (IQNA) babban sakakaren kungiyar Hizbullah ya bayyana siyasar Amurka da cewa ta ginu ne kan manufa guda, amma Trump yana da mummunar manufa a kan al’ummomin duniya.

Sayyid Hassan Nasrulalh ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a daren jiya, dangane da zagayowar ranar da Ahmad Qasir, wani dan gwagwarmaya a kasar Lebanon ya tarwatsa sansanin sojojin yahudawan Isra’ila da suke mamaye da kasar Lebanon a lokacin, inda ya halaka 89 daga cikin sojojin yahudawan.

Sayyid Nasrullah ya ce, babu wani banbanci a tsakanin dukkanin gwamnatocin Amurka kan siyasar kasar dangane da Isra’ila, kuma duk wani shugaban Amurka da zai zo dole ne ya aiwatar da wannan siyasa, wajen taimaka ma Isra’ila da dukkanin abin da take bukata domin ci gaba da murkushe al’ummar Falastinu, da kuma zama babbar barazana a yankin gabas ta tsakiya.

Ya ce tabbas ya yi farin ciki da Donald Trump ya sha kasa a zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Amurka, kasantuwar Trump shi ne shugaba mafi muni a Amurka a tarihin baya-bayan nan, da yake da mummunar manufa a kan al’ummomin duniya, da hakan ya hada har da kan kasashe kawayen Amurka, inda yake cin zarafinsu da wulakanta su da kaskantar su.

Haka nan kuma Sayyid Nasrullah ya yi ishara da daya daga cikin ayyuka mafi muni da Trump ya aikata a kan masu gwagwarmaya da zaluncin duniya a wannan lokaci, shi ne kisan janar Wasim Sulamaini da kuma Abu Mahdi Almuhandis., da kuma mara baya ga manyan azzaluman mahukunta ‘yan kama karya a kasashen yankin gabas ta tsakiya.

Sayyid Nasrullah ya bayyana Trump da cewa yana da girman kai da dagawa da jin cewa yafi kowa a duniya, wanda hakan ne ma ya sanya shi yin turjiya wajen kin amincewa da sakamkaon zaben Amurka inda ya sha kayi, domin a tunaninsa shi yafi karfin a kayar da shi, domin baya daukar kaskanci.

A daya bangaren kuma ya jinjina wa kawayen Hizbullah musamman ma bangarorin siyasa na cikin kasar Lebanon da suke kawance da kungiyar, wanda sakamakon haka ne ma gwamnatin Amurka ta kakaba wa wasu takunkumi da kuma yin matsin lamba a kansu.

Na baya-bayan nan shi ne tsohon ministan harkokin wajen kasar Jubran Bassil, wand a cikin wannan mako Amurka ta kakaba masa takunkumi, saboda yaki yanke alaka da Hizbullah.

Sayyid Nasrullah ya ce wace doka ce ta duniya ta baiwa Amurka damar ta zama ita ce mai hukunta mutane a duniya, ta yadda za ta kira wasu ‘yan ta’adda saboda dalilai na siyasa, alhali ita ce kan gaba wajen tafka ayyukan ta’addanci a duniya, wanda abin da ta yi a Iraki, Syria, Afghanistan da kuma taimaka ma masu kisan mata da kananan yara a Yemen ya isa babban misali kan hakan.

 

3934730

 

captcha