IQNA

Macron A Hubbaren Imam Musa Kazem (AS) A Bagadaza Iraki

16:42 - August 29, 2021
Lambar Labari: 3486250
Tehran (IQNA) shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci hubbaren Imam Musa Kazem (AS) da ke yankin Kazimiyya a birnin Bagadaza na Iraki.

Kamfanin dillancin labaran kasar Iraki INA ya bayar da rahoton cewa, da jijjifin safiyar yau Lahadi, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron tare da rakiyar Firayi ministan kasar Iraki Musatafa Kazemi ya ziyarci hubbaren Imam Musa Kazem (AS) da ke yankin Kazimiyya a birnin Bagadaza.

Ofishin firayi ministan kasar Iraki ya fitar da bayanin cewa, Macron tare da rakiyar firayi minista Alkazimi da kuam sauran jami'an da suke tare da su sun ziyarci hubbarori biyu na Imam Kazim da Imam Jawad (AS).

Wannan na zuwa ne bayan kammala taron da aka gudanar a jiya a kasar Iraki wanda ya samu halartar shugabannin kasashe da manyan jami'ai, kan tabbatar da zaman lafiya da yin aiki tare tsakanin kasashen yankin.

Shugaban kasar ta Faransa yana daga cikin wadanad suka halarci wannan zaman taro, inda aka tattauna batutuwa da dama da suke ci ma yankin gabas ta tsakiya tuwo a kwarya.

 

 

 

3993608

 

captcha