Harin ya faru ne a masallacin Imam Sahib dake lardin Kunduz, inda masu ibadar da dama suka rasa rayukansu ciki har da yara, kamar yadda kakakin gwamnatin Taliban Zabihullah Mujahid, ya wallafa a shafinsa na tuwita.
Harin na jiya Juma’a na zuwa ne kwana guda bayan da kungiyar IS, ta dauki alhakin kai wasu munnannen hare hare kan wasu masallatai na ‘yan shi’a dake yankin, wandanda sukayi sanadin mutuwar mutane akalla 16 da kuma raunata wasu da dama a birnin Mazar-i-Sharif dake arewacin kasar.
A watannin baya bayan nan, kasar ta Afganistan, ta sha fuskantar jerin hare-haren ta’addanci daga kungiyar mai da’awar kafa daular musulunci ta IS, mai adawa da gwamnatin rikon kwarya ta Taliban.
Iran, dake makobtaka da kasar ta Afghanistan, ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajenta ta nuna matukar damuwarta game da yawaitar hare haren da tda danganta da na rashin imani da tausayi musamman a wannan wata na Ramadana, da al’ummar musulmi ke taruwa a masallatai domin neman rahamar ubangiji.