IQNA

An zargi wani matashi mai amfani kafofin sada zumunta a Aljeriya da wulakanta masallaci

13:27 - April 27, 2023
Lambar Labari: 3489047
Tehran (IQNA) Ayyukan wani matashi mai amfani da kafofin sada zumunta na zamani a Aljeriya, wanda ya saka wakar rap a lokacin da yake shiga masallaci, ya gamu da martani na masu amfani da yanar gizo a wannan kasa.

A rahoton Arabi 21, an ambaci sunan Marwan Al-Batni, matashin dan kasar Algeria mai gabatar da barkwanci  a shafukan sada zumunta a Algeria bayan fitar da wani faifan bidiyo daga cikin masallaci.

A cikin wannan faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Tik Tok, Al-Batni ya shiga wani masallaci an  fara karatun Al-Qur'ani. Yayin da ake karatun kur'ani, ana iya jin muryar wani mawaƙin rap na yamma a bayan wannan faifan. An soki wakokin da aka yi amfani da su a cikin wannan faifan, wanda masu amfani da shafukan sada zumunta ke ganin bai dace da masallacin ba.

Wannan mataki na Marwan Al-Batni ya gamu da cikas da suka kuma masu amfani da kafofin sada zumunta na wannan kasa sun bukaci mahukuntan Aljeriya da su fara gudanar da bincike kan wannan lamari tare da da daukar mataki kan wannan mataki.

Akwai dai wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba na cewa jami'an tsaro sun kama shi. Wannan matashin dan kasar Aljeriya yana da mabiya sama da miliyan uku a dandalin sada zumunta na Tik Tok, kuma bidiyon da ya yi a wurin ya samu kallo daga mutane sama da miliyan 43.

 

 

4136583

 

captcha