IQNA

Ministan harkokin wajen Rasha ya yi Allah wadai da yaduwar kyamar Musulunci a Turai

15:42 - September 24, 2023
Lambar Labari: 3489867
New York (IQNA) Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, ya soki yadda ake ci gaba da nuna wariyar launin fata a kasashen yammacin duniya, da daidaitawa da yaduwar kyamar Musulunci da rashin hakuri da addini da kimarsa.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Masdar cewa, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya yi gargadi kan wariyar launin fata a yammacin jiya Asabar, inda ya bayyana cewa: Har yanzu kasashen yammacin duniya suna daukar kansu sama da sauran bil’adama.

Lavrov ya yi ishara da kalaman batanci na shugaban hukumar diflomasiyya ta Turai, Josep Borrell, wanda ya ce a zahiri: Turai wani lambu ne da ke kewaye da wani daji.

Ministan Harkokin Wajen Rasha ya jaddada cewa: Burrell ba ya jin kunyar yaduwar kyamar Musulunci da sauran nau'o'in rashin haƙuri ga tsoffin dabi'un duk addinan duniya a cikin wannan "lambu".

Ya kara da cewa: Kona kur'ani, cin mutuncin Attaura, tsananta wa limaman Orthodox da cutar da mabiya addini abu ne da ya zama ruwan dare a Turai.

Borrell ya ce Tarayyar Turai ta kasance "mai ciyawa a cikin maharbi" amma dole ne ta "farka" saboda rikici a Ukraine.

A ranar 13 ga Oktoba, yayin bude Cibiyar Diflomasiya ta Turai a Bruges, Belgium, Burrell ya ce "mabambantan" Turai "lambu ne" kuma duniya da ke kewaye da ita "daji". Hakan ya haifar da cece-ku-ce a kasashen Turai da ma duniya baki daya, kuma a karshe ya tilasta wa sashen harkokin wajen na kasashen Turai da jami'an diflomasiyyar Turai su nemi gafara, Sun bayyana wadannan kalamai da cewa sun sabawa tsarin manufofin kungiyar EU kuma sakamakon rashin fahimta.

 

4170836

 

captcha