IQNA

Kotun Indiya ta ba wa mabiya addinin Hindu izinin yin ibada a masallacin musulmi mai tarihi

21:02 - February 01, 2024
Lambar Labari: 3490576
IQNA - Wata kotu a Indiya a ranar Laraba ta yanke hukuncin cewa za a bar mabiya addinin Hindu su yi ibada a masallacin Gyanvapi mai dimbin tarihi da ke gundumar Varanasi ta Uttar Pradesh.

A cewar jaridar Hindustan Times; Kotun Varanasi ta yanke shawarar barin mabiya addinin Hindu su yi ibada a cikin ginin masallacin Gyanvapi mai tarihi.

A cewar jaridar, kotun ta kuma baiwa mahukuntan masallacin wa'adin mako guda da su samar da sharuddan da suka dace ga mabiya addinin Hindus su yi ibada a cikin masallacin.

Kotun Indiya ta fara sauraron wannan karar ne a watan Satumbar 2022.

A halin da ake ciki dai mahukuntan masallacin na shirin mika karar zuwa kotun kolin Indiya.

Tun da farko, wasu kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin addinin Hindu sun yi ikirarin cewa an gina masallacin Gyanvapi a wani bangare na haikalin Hindu da aka lalata a karni na 17.

Masu tsattsauran ra'ayin addinin Hindu sun kuma yi ikirarin cewa an gina wasu masallatai da dama a kasar, kamar masallacin Gyanvapi. 

 

 

 

4197389

 

Abubuwan Da Ya Shafa: masallaci mahukunta mabiya addini Hindus
captcha