IQNA

An kashe mutane da dama a wani hari da aka kai a wani masallaci a Burkina Faso

16:59 - February 27, 2024
Lambar Labari: 3490717
IQNA - Bayan wasu mutane dauke da makamai sun kai hari a wani masallaci a Burkina Faso, an kashe musulmi da dama da ke wannan masallaci.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Rai Alyoum cewa, an kashe musulmi da dama a ranar Lahadin da ta gabata a wani babban harin da aka kai a wani masallaci da ke Nathiaboani a gabashin kasar Burkina Faso. A halin da ake ciki kuma, a wannan rana, an sake kai wani harin zubar da jini a kan mabiya darikar Katolika da suka taru a cocin.

Wata majiyar tsaro ta ce dangane da haka: Wasu mahara dauke da makamai sun kai hari a wani masallaci a Natyabowani a ranar Lahadi da misalin karfe biyar na safe (lokacin gida) inda suka kashe mutane da dama.

A wata wayar tarho, daya daga cikin mazauna garin ya sanar da harin da aka kai a wannan masallacin: “Wadanda aka kashe duk musulmi ne, yawancinsu maza ne da suka taru a masallacin domin yin sallah.

Wata majiyar kuma ta ce dangane da haka: 'Yan ta'adda sun shiga cikin garin da sassafe, inda suka kewaye masallacin, suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi, wanda a sakamakon haka ne aka harbe wasu da dama daga cikin masallatan ciki har da daya daga cikin malaman addini. 

Garin na Nathiabwani yana da tazarar kilomita 60 kudu da Fada Ngorma, tsakiyar yankin gabas, wanda tun a shekara ta 2018 ne kungiyoyi masu dauke da makamai ke kai hare-hare akai-akai.

Burkina Faso dai na karkashin mulkin soja ne da suka kwace mulki a shekarar 2022. Tun daga shekara ta 2015, kasar nan ta fuskanci tashe-tashen hankula na kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qaeda da ISIS, inda aka kashe kusan mutane 20,000 tare da raba sama da mutane miliyan biyu da muhallansu.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4202110

Abubuwan Da Ya Shafa: hari masallaci malamai addini darikar katolika
captcha