Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Khalij cewa, daga Los Angeles zuwa New York, Austin, Boston, Chicago da Atlanta, kungiyar dalibai masu goyon bayan Falasdinu na kara fadada a Amurka.
Kwanaki da dama ana gudanar da zanga-zanga a manyan jami'o'in duniya kamar Harvard, Yale, Columbia da Princeton. A halin da ake ciki dai hukumomi na barazanar tura jami'an tsaro domin tarwatsa su.
Kwanaki da dama, ana maimaita wannan yanayin a yankuna daban-daban na Amurka; Dalibai sun kafa tantuna a harabar jami'o'insu tare da yin Allah wadai da goyon bayan sojojin Amurka ga Isra'ila da laifukan da wannan gwamnati ke yi a zirin Gaza. Wadannan zanga-zangar galibi suna fuskantar harin da 'yan sandan kwantar da tarzoma suka kai musu.
Cibiyoyin Amurka da mambobin Majalisar, karkashin jagorancin Kakakin Majalisar Wakilai, Mike Johnson, sun zargi mahalarta zanga-zangar da " kyamar Yahudawa". A gefe guda kuma sun bukaci Isra'ila da ta daina kashe Falasdinawa fararen hula a Gaza.
Bisa labarin da kamfanonin dillancin labaru na kasa da kasa suka bayar da kuma wasu faifan bidiyo a shafukan sada zumunta sun nuna jami'an tsaron Amurka sun kuma kai hari a harabar jami'o'i da dama, inda suka far wa daruruwan dalibai, masu bincike da malaman jami'o'i tare da kame da dama daga cikinsu.
Daliban Yahudawa a Jami'ar Columbia sun yi watsi da ikirarin cewa zanga-zangar goyon bayan Falasdinu ana daukarta a matsayin barazana ta kyamar Yahudawa tare da jaddada cewa jami'an jami'ar ba gaskiya suke fada ba.