IQNA

Kotun Holland Ta Yi Umarni Da A Gina Ma Musulmi Makaranta

17:29 - July 27, 2017
Lambar Labari: 3481741
Bangaren kasa da kasa, Kotun koli a kasar Holland ta bayar da umarni da a gina ma musulmi makarantar sakandare a cikin birnin Amstardam fadar mulkin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai na World Bulletin ya bayar da rahoton cewa, kotun kolin kasar Holland ta bayar da umarnin fara ginin wannan makaranta daga wata mai kamawa.

Tun a cikin shekara ta 2011 ce dai cibiyar musulmin kasar Holland mazauna birnin Amstardam suka gabatar da bukatar neman a gina musu makaranta wadda za ta rika koyar da boko da kuma darussan muslunci, amma ma'aikatar ilimi ta kasar ta yi watsi da batun.

A cikin shekara ta 2015 wannan cibiya tabi kadun lamarin ta hanyar shari'a, inda a jiya kotun kolin kasar ta Holland ta amince da wannan bukata, ta bayyana hakan da cewa yana akan doka, haka nan kuma kotun ta umarci ma'aikatar ilimi ta kasar Holand ta fara aikin ginin wannan makaranta daga wata mai kamawa.

A fadin kasar Holland makaranta daya ce musulmi suka mallaka, wadda take a birnin Rotterdam, wato kwalejin Ibn Sina, inda ake koyar da darussa na boko da kuma na addinin muslunci.

3623590


captcha