IQNA

Wasikar Mata Da Suka Samu Lambar Yabo Ta Nobel Ga Shugabar Myanmar

20:58 - September 14, 2017
Lambar Labari: 3481895
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin mata da suka samu labar yabo ta zaman lafiya ta nobel sun rubuta wasika zuwa ga shugabar gwamnatin Myanmar suna Allah wadai da matakin da ta dauka kan kisan msuulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Anatoly AA cewa, sakamakon gum da bakinta kan kisan da sojojin gwamnati da kuma ‘yan addinin buda suke yi wa musulmi ‘yan kabilar Rohingya Myanmar, shugabar gwamnatin kasar na ci gaba da sha kakkausar daga koina cikin fadin duniya.

Kimanin mata 5 daga cikin matan da suka samu lambar yabo ta zaman lafiya ta nobel, sun rubuta mata wata wasika, inda suke bayyan takaicinsu kana bin da yake faruwa akasarta na kisan bil adama saboda banbancin akida.

A cikin wasikar matan sun bayyana cewa, wannan abin da yake faruwa na kisan kiyashia kan msuulmi ‘yan kabilar Rohingya yayi hannun riga da dimukradiyyar da kika share tsawon shekaru kina gwagwarmaya akanta, domin kuwa hakan shi ma hakan zalnci ne irin wanda kika yi yaki da shi a halin yanzu ake yi a karkashin mulkinki.

A wani bangaren wasikar an bayyana cewa, Aung Suu Kyi ba ki yi magana kana bin da yake faruwa ba, har sai an kasha dubbai masu yawa daga ‘yan kabilar Roohingya, a lokacin ne za ki yi magana da a daina kisan kiyashi a kansu.

3641976

captcha