IQNA

An Tuna Da Malamin Kur'ani A Radiyon Alkahira

17:55 - September 16, 2017
Lambar Labari: 3481900
Bangaren kasa da kasa, Radio Sautul arabi an gudanar da taron tunawa da babban malamin addinin kuma makarancin kur'ani mai tsarki Sheikh Mahmud Khalil Husri a radiyon kur'ani na Masar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na veto cewa, Yasmin Husri diyar babban malamin ta kasance daga cikin masu halartar taron.

Ta bayyana cewa hakika mahaifinta ya kasance mutum ne mai bayar da matukar muhimamnci ga lamarin kur'ani mai tsarkia cikin rayuwarsa, wanda hakan ya sanya ya tasirantu matuka da kur'ani.

Baya ga haka kuma a lokacin da yake karatu yak an kasancea cikin natsuwa, ta yadda bashi kawai ba hatta ma masu saurarensa karatun yakan yi tasiri a kansu.

Da dama dagacikin mutane kasar Masar suna daukar Sheikh Khalil Husri a matsayin mutum mai girma da kima a bangaren kur'ani mai tsarki.

Wannan babban malami dai ya kasance daya daga cikin wasdanda suka fara gudanar da karatun kur'ani da sautinsa mai kyau a gidan radiyo na kur'ani na kasar Masar.

Ya kasance daga cikin wadanda suak hardace kur'ani yana da karacin shekaru matuka, ta yadda yakan shiga cikin manyan makaranta da mahardata kuma ya goga da su a dukkanin bangarori na gasar kur'ani mai tsarki.

A cikin shekara ta 1944 ya zo a matsayin makaranci kuma mahardaci na daya a gasar kur'ani ta radiyon kur'ani da ake gudanarwa, inda aka sanar da shi a matsayin makaranci na daya Masar.

3642464


captcha