IQNA

Taron Karawa Juna Sani Kan Addinai A Birtaniya

20:28 - November 15, 2017
Lambar Labari: 3482103
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da taron karawa juna sani a birnin York an kasar Birtaniya wanda mabiya addinai daban-daban za su halarta.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarta cewa a cikin wanann makon za a gudanar da taron karawa juna sani a birnin York an kasar Birtaniya wanda mabiya addinai za su halarta domin gabatar da kasidu.

Bayanin ya ce an gayyaci masana 70 daga bangarori daban-daban da kuma addinai, da suka hada da kiristanci, muslunci yahudanci, sik, buda da sauransu.

A zaman taron masana za su gabatar da kasidu da suke dauke da mahngarsu kan addinai da kuma yadda za akarfafa zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin dukkanin mabiya addinai na duniya.

Mark Kasenz daya daga cikin masana addinin kiristanci ya bayyana cewa, wajibi ne a karfafa dukkanin hanyoyin da za su taimaka wajen samun zaman lafiya da fahimtar juna atsakanin dukkancin addinai.

Wannan taron zai mayar da hankali ne kan halin da duniyar yau take ciki da kuma manyan kalubale da take fusknata, tare da gabatar da shawarwari kan hanyoyin da malaman addinai za su dauka domin fuskantar wannan kalu bale.

3663607


captcha