Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, mabiya mazhabar shi’ar ahlul bait (AS) sun gudanar da tarukan tunawa da zagayowar ranar Ashura a kasar Sweden.
Bayanin ya ce kamar kowace shekara an fito a kan tituna dauke da tutoci da kwalaye da aka yi rubutu kansu da ke bayyana abin da ya faru da Imam Hussain (AS) da kuma zuriyar manzon Allah a rana Ashura.
Bayan nan kuma an gudanar da jawabai inda muuslmi da dama suka taru mabiya mazhabar shi’a da ma wadanda ba su ba, har da wasu daga cikin turawan kasar, inda suka saurari jawaban da aka gudanar kan wannan rana.