Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, faifan bidiyo na wata ‘yar Falasdinu a zirin Gaza da ke kokarin kwantar da hankalin ‘yar uwarta ta hanyar karanta ayoyin suratu Malik kafin ta yi barci, ya samu kulawa daga masu amfani da shafukan sada zumunta.